Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soyayya Tafi Dadi Da Saurayi Dan-Zamani


facebook
facebook

Ganin yadda hanyoyin sadarwar zamani ke shafar rayuwar al’uma da ma duniya gabaki daya, lallai mutane na iya yin kusan komi ta hanyar yanar gizo. zaka iya neman aiki, ko makaranta harma kayi karatun digirgir ba tare da ka je wani aji ba, kuma zaka iya yin sayayyar kaya da sauran abubuwa da dama duk ta wannan hanya. Wasu ma ta hanyar yanar gizo suka hadu da abokan soyayyar su har suka kaiga yin aure.

Ko ka taba jin labarin wasu ma’aurata daga kasashe daban daban da suka hadu ta yanar gizo kuma a yau suna tare da juna? Wannan sabon shirin akan soyayyar zamani a game da kai mai sauraro aka shirya shi, kuma lallai saboda kai aka hada shi. Ku rubuto mana ra’ayoyin ku ta shafin mu na dandalinvoafacebook domin yadda kuka ji dadin wannan sabon shirin da kuma tafka mahawara. Ta wacce hanya magabatan mu suka hadu har suka yi aure suka haife mu?

A wannan zamanin jama’a da dama sun hada zumunci mai karfin gaske ta hanyar facebook, kuma har ila yau muna jin labaran auratayya da kuma samartaka da sauran su duk ta hanayar facebook. Kana ko kina iya kira aika sako a rubuce ko text a takaice, ta hanyar facebook. A shafin ko wane mai anfani da facebook, kana ko kina iya ganin bayanai dangane da shi koi ta, misali inda tayi ko yayi makaranta, inda mai shafin yak e aiki ko sana’a da ma yawan abokan da mai shafin yak e da su.

Wani lokacin ma kana iya ganin abokan abokan mai nshafin, wanda zai iya ba mai bincike damar samin Karin bayanai akan mai shafin. Hakika yana da matukar muhimmanci samun masaniya akan wanda mutum ke neman bayanan sa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG