Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soyayyar Zamani Tafi Dadi Ta Yanar Gizo


Wanna shirin da zamu fara gabatar wa daga yau, zai dinga zuwan muku ne a kowace ranar juma’a da asabar. Shirin, zai dinga duba yadda matasa maza da mata ke gudanar da rayuwar su ta yau da kullun a bangaren soyayya,da zaman takewa, da kuma tunanatar da juna duk a wanna zamani da muke ciki, a wannan karni na Ashirin da daya. Da karon farko zamu fara duba wai wace irin rawa, shafufukan yanar gizo ke takawa a rayuwa matasa?

Yawancin jama’a suna anfani da internet/yanar gizo a kowacce rana wadanda yawanci matasa ne a duk fadin duniya, kuma suna anfani da shafukan sadarwa daga irin su Twiter har zuwa su Instagram, har ma da facebook da sauran su.

A wannan lokacin, yawancin mutane sun dogara ne akan hanyoyin sadarwar yanar gizo domin sanin yanayin da duniyar ta ke ciki da kuma sauran al’umar duniya.

Jama’a na haduwa da abokai da suka dade basu ga juna ba, ko kuma su ka ji daga gare suba ta hanyar facebook, har ma suna iya ganin irin abubuwan da ke faruwa da su alokaci guda, kuma suna iya cigaba da yada zumunci a tsakani su, kai harma sana iya tofa albarkacin bakin su dangane da irin hotunan da mai shafin ya lika a shafin sa. Jama’a na iya karanta labarum abubuwan da ke gudana da ‘yan uwa da abokai duk inda suke a fadin duniya. Kafar yada zumunta ta zamani ta sa gabaki daya jama’a sun zama tamkar ‘yan al’uma daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG