Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pandar Da Tafi Kowacce Girma Ta Haifi Tagwaye


Panda
Panda

Panda mai suna Mei Xiang wata dabba ce, wace ake samunta a mafi yawancin kasashen yankin China. Wanna dabar, ita ce tafi kowace girma a duniya, jiya Lahadi ta haifi tagwaye.

Masu kula da gidan namun daji sun tabbatar da lafiyar uwar da ‘yayan. A zuwa yanzu dai basu iya tan-tan ce ko wane irin jinsi ta Haifa ba, amma nan gaba kadan zasu iya gane mace ne ko namiji.

A tabakin shugaban gidan Zoo din, Mei Xiang. Dabba ce mai hankali don haka basu sa ran zata cutar da ‘yayan nata, duk dai da cewar ‘yayan sunyi kanana.

A watan Aprilu da yagabata akayi ma wanna dabbar allura, inda aka hada kwanta da na wasu mazan Panda biyu, sai aka samu ‘yaya. Amma an dauki kwayayen Pandoji biyu ne, aka samata don haka masana sun ce za’a binciki ko wadanne daga cikin biyun ne uban ‘yayan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG