Jennifer Lawrence ta zamo jarumar da ta fi kowace jaruma samun kudi mai tsoka a cikin watanni 12 da suka shige. Mujallar Forbes ta ce Jennifer Lawrence ta samu zun zurutun kudi dala miliyan 52, kimanin Naira miliyan dubu 10 har da canjin Naira miliyan 400 a kai.
Amma kuma, abin mamaki shine bambancin dake akwai a tsakanin jarumar da ta fi samun kudi a fina-finan Hollywood, da kuma jarumi namiji da ya fi samun kudi.
A bana, jarumin da yafi samun kudi shine Robert Downey Jr wanda yayi fim din nan mai suna Iron Man, wanda kuma abinda ya samu ya zarce na Jennifer Lawrence da dala miliyan 28, watau Naira miliyan dubu 5 da 600, inda ya samu dala miliyan 80, ko Naira miliyan dubu 16.
Wadda ta zo ta biyu a bangaren mata jarumai it ace Scarlett Johansson wadda ta samu dala miliyan 35 da rabi, ko Naira miliyan dubu 7 da canjin naira miliyan dari daya a kai. A bangaren maza jarumai kuwa, shahararren jarumi Jackie Chan shine na biyu a cikin watanni 12 da suka shige, inda shi kuma ya kalmasa dala miliyan 50 ya jefa a aljihunsa, watau kimanin Naira miliyan dubu 10, tsaba.
Kamar yadda masu sanya idanu kan wannan harka ta fina-finan Hollywood ke fadi, abinda ya fi bada mamaki, duk da cewa kusan rawa guda jarumai maza da mata ke takawa a fina-finai, akwai wagegen gibi a tsakanin abinda suka samu. Yayin da mata hudu ne kawai cikin jerin jarumai mata suka iya samun kudin da ya zarce dala miliyan 20 a watanni 12 da suka shige, maza har guda 21 suka samu dala miliyan 20 ko fiye da haka.
Haka kuma duk da cewa a karon farko an auna fina-finan kasashen waje, ba wai jaruman kasashen waje kawai dake fita cikin fina-finan Amurka na Hollywood ba, mace day ace kawai ‘yar kasar waje ta shiga cikin wannan jerin, watau wata jaruma ‘yar kasar China mai suna Bingbing Fan, wadda ta fito a zaman Blink cikin fim din X-Men: Days of Future Past.
A bangaren maza, jaruman kasashen waje da dama sun samu shiga cikinsu har da Amitabh Bacchan, Salman Khan, Ashkay Kumar, Shahrukhkhan da kuma Ranbir Kapoor.
Domin ganin cikakken jerin jaruman da kuma kudaden da suka samu, a duba shafinmu na www.dandalinvoa.com