Yamal ya kasance muhimmin dan wasa a nasarar Sifaniya a gasar cin kofin Turai a bana.
Washington D.C. —
Dan wasan Barcelona Lamine Yamal ya bar tawagar kasarsa ta Sifaniya bayan ya ji rauni a kafarsa ta hagu.
Yamal bai zai buga wasan gida na Sifaniya a gasar Nations League da za ta kara da Serbia a ranar Talata ba.
A rana guda bayan dan wasan gaban mai shekara 17 ya taimaka wa Sifaniya ta doke Denmark da ci 1-0, kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya ta ce a ranar Lahadi gwaje-gwaje sun nuna tauraron Barcelona ya ji rauni a kafarsa, kuma an aika shi ya koma kulob dinsa don guje wa " hadarin jin mummunan rauni."
Yamal ya kasance muhimmin dan wasa a nasarar Sifaniya a gasar cin kofin Turai a bana.
Kocin Sifaniya, Luis de la Fuente, ya kira dan wasan Atletico Madrid, Rodrigo Riquelme, domin ya maye gurbin Yamal.