Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona, Real Madrid Za Su Koma Filin Daga Babu Wasu ‘Yan wasa


Spain Soccer La Liga
Spain Soccer La Liga

Ita dai Girona na ci gaba da jagorantar teburin gasar ta La Liga yayin da take shirin karawa da Athletico Bilbao a ranar Litinin.

Barcelona da Real Madrid za su kara a wasanni daban-daban a karshen makon nan yayin da suke fama da ‘yan wasa marasa lafiya.

‘Yan wasan kungiyoin biyu da ke jiny sun ji rauni ne a wasannin kasashensu da suk buga.

Barcelona za ta kai wa Rayo Vallecano ziyarar bayan da dan wasanta na tsakiya Gavi ke fama da rauni a gwiwa wanda ya ji lokacin yana buga wa kasar ta Sifaniya wasa.

Madrid kuwa za ta kai wa Cadiz ziyarar yayin da take laluben wanda zai maye gurbin Vinicius Junior da kuma dan wasan tsakiya Eduardo Camavinga.

Ita dai Girona na ci gaba da jagorantar teburin gasar ta La Liga yayin da take shirin karawa da Athletico Bilbao a ranar Litinin.

Kungiyar ta Girona da ta shammaci jama’a na gaban Madrid da maki biyu yayin da ta ba Barcelona tazarar maki hudu.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG