Lauyoyin dan wasan Brazil Dani Alves sun ce za su daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke masa bayan da ta same shi da laifin aikata fyade.
A ranar Alhamis kotun ta samu Alves da laifin yi wa wata mata fyade a wani gidan rawa a Barcelona, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu da watanni shida a gidan yari.
Kotun Lardin Barcelona ta yanke wa tsohon dan wasan na Brazil da Barcelona dan shekaru 40 hukuncin ne bisa laifin yin fyade a ranar 31 ga Disamba, 2022.
Kotun ta yi la’akkari da cewa matar ba ta amincewa Alves ya sadu da ita ba, abin da ke nuni da cewa fyade ya yi mata.
Har ila yau, Kotun ta kuma umurci Alves da ya biya diyyar euro 150,000 ga matar, da kuma haramta masa zuwa gidan ta, ko kuma wurin aikin ta, ko kuma yin magana da ita ta kowace hanya har tsawon shekaru tara.
David Saenz wanda yana daya daga cikin lauyoyin da suka kare matar, ya ce, "sun gamsu da hukuncin."
Dandalin Mu Tattauna