A wata wasika da ya rubutawa majalisar dattawa gwamnan babban bankin Najeriya Lamido Sanusi Lamido ya ce wasu makudan kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka miliyan dubu arba'in da takwas sun salwanta daga baitulmalin kasar.
WASHINGTON, DC —
Wasikar Gwamnan Babban Bankin Najeriya Lamido Sanusi Lamido dangane da salwantar wasu kudade da suka ninka kudin kasafin kasar har na shekara biyu ta tayarwa 'yan majalisar hankali lamarin da ya sa suka kafa kwamitin binciken gaggawa ya binciko maganar cikin mako daya.
Jiya majalisar ta yi wata muhawara mai zafi kan wasikar gwmnan bankin.Kudin da wasikarsa ta ambato sun salwanta daga baitulmalin kasar sun kai nera tiriliyan takwas ko nera miliyan miliyan takwas ko kuma Dalar Amurka miliyan dubu arba'in da takwas da digo tara. Wasikar ta gwamnan ta ce an samu kudin ne daga gurbataccen man fetur da Najeriya ta sayar sakanin farkon shekarar 2012 zuwa tsakiyar wannan shekarar ta 2013.
Jin nauyin yawan kudaden ya sa majalisar ta dorawa kwamitin dinta na kudi nauyin yin bincike ba tare da bata lokaci ba a kan wadannan makuden kudade da ake zargin sun batar da sawu.
Adamu Ibrahim Gumba yana cikin kwamitin da aka dorawa nauyin binciken ya ce kudin sun shigo babban bankin Najeriya yanzu aikinsu ne su bincika yaya aka yi da kudaden. Ina suka je kuma wa ya bayar da izinin fitar da su. Ya ce kwamitin dake karkashin tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi ba zai yi wasa da aikin ba. Ya ce da yaddar Allah zasu yi kokari su gano inda aka yi da kudaden. Idan sun gama bincike zasu baiwa majalisar dattawa sakamakon bincikensu kana ita ma ta gayawa duniya gaba daya.
Duk da kokarin da Sanato Adamu Ibrahim Gumba ya ce kwamitin zai yi wurin gano sahihiyar gaskiyar maganar abokin aikinsa Sanato Bukar Ibrahim na jam'iyyar adawa ta APC ya ce wajibi ne majalisar ta yi rawar gani a wannan karon. Ya ce duk da maganganun sace-sace da ake yi a kasar ba'a taba tafka sata irin wannan ba sabili da haka babu yadda za'a bar maganar ta mutu kamar yadda aka saba yi.
Daga shiyar majalisar wakilai Aliyu Gebi ya bayyana ra'ayinsa inda ya yaba da matakin da gwamnan babban bankin Lamido Sanusi Lamido ya dauka na bayyana wannan badakalar. Ya ce su a majalisar wakilai sun godewa gwamnan domin ya fitar masu da kitse a ruwa. Da ana ganin 'yan arewa tamkar tunkiyoyi ne wadanda basu san abun da suke yi ba, sai gashi yau an wayi gari dan arewa ya bankado wannan badakalar. Da ya shigo bankin ya shiga gyara kuma ya sha nuna irin barnar da aka yi a bankin da rashin sa ido kan bankuna lamarin da ya kai ga dimbin asarar da mutane suka yi.
Medina Dauda nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5