An damkawa kwamitin binciken karkashin jagorancin Ibrahim Nikau, alhakin “karba, bincike da nazarin duk wani bayani, ko kuka, ko kara ko zargi dangane da wuraren da ake tsare mutane cikinsu haka siddan a duk fadin Najeriya.”
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a fadin duniya, cikinsu har da “Human Rights Watch” da “Amnesty International” sun bayyana damuwa a kan yadda ake keta hakkin jama'a a wuraren da ake tsare mutane, musamman ma a wuraren da ake tsare wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne.
Kwanakin baya ne shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayarda sanarwar sakin kudi fiye da Naira Biliyan daya domin yin kwaskwarima a barikin Giwa dake Maiduguri da wasu wuraren da sojoji suke yin amfani da su wajen tsare mutanen da suke zaton 'yan Boko Haram ne.
Rundunar sojojin Najeriya dai ta furta cewa da gaske ne tana tsare da daruruwan mutanen da ake zaton 'yan Boko Haram ne ba tare da an gurfanar da su a gaban shari'a ba.
Haka kuma an ba wannan kwamiti na hukumar kare hakkin bil Adama ikon kai ziyara, da dubawa ko nazarin duk wuraren da ake tsare mutane cikinsu a duk fadin Najeriya, ko da wanene yake gudanar da su.