Gwamnan babban bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi ya ce gwamnatin tarayya a shirye take ta taimakawa jihohin arewa maso gabas domin bunkasa tattalin arzikinsu yayin da ya gabatar da kasidarsa a wurin taron habbaka tattalin arzikin yankin. Malam Sanusi ya nuna takaicinsa kan rashin bankunan al'umma a jihohin shida.
Dangane da irin taimakon da babban bankin Najeriya zai baiwa jihohin, Malam Sanusi ya ce taimakon shi ne canza dokoki da ka'idodin kafa bankunan al'umma yadda za'a bar gwamnatoci su nemi izinin kafasu. Ya ce idan suka nema za'a basu izinin yin hakan.
Bincike ya nuna cewa shiyar arewa maso gabas mai jihohi shida wato Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe nada bankunan al'umma 34 kacal ne cikin sama da 900 dake kasar Najeriya gaba daya. Kasar nada shiyoyi shida ne kawai. Domin haka ya kamata a ce shiyar nada bankunan al'umma akalla 100 in ba 150 ba.Abun takaici kuma shi ne jihar Yobe bankin al'umma daya kacal take da shi.An tambayi kwamishanan noma na jihar Yobe Malam Idi Barde Gubana ko wane mataki zasu dauka sai ya ce su da suka halarci taron daga jihar sun tattauna sun kuma ga alfanun bankin. Idan sun koma gida zasu ba gwamnan jihar shawara ta yadda kowace karamar hukuma a jihar zata kafa daya akalla.
A nashi bayanin Alhaji Isa Masindi ya jaddadawa gwamnonin jihohin shida mahimmancin cin gajiyar kafa bankunan al'umma. Ya ce akwai kudin da aka fitar na kafa bankin talakawa inda Jihar Taraba ta samu nera miliyan dubu. Babu abun da ya hana sauran jihohin su shirya su kafa nasu bankunan al'umma domin su samu tallafin.Ya ce bankin al'umma na talakawa ne kuma shi ne zai iya taimaka masu.
Tuni jihar Kano ta ci gajiyar irin wannan tallafin na nera miliyan dubu dari biyu lamarin da ya dada habbaka tattalin arzikin jihar.
Sa'adatu Fawu Mohammed nada karin bayani.