Hukumar Tsaro ta jihar mai suna "Operation Rainbow" ita ce ta shirya horon kan dabarun da matasan zasu iya gano da shawo kan ta'adanci kafin ya faru. Horon ya hada da koya masu yadda zasu shaidawa jami'an tsaro kafin lamarin ya auku.
Shugaban hukumar operation rainbow a jihar Filato Air Vice Marshall Bala Danbaba mai ritaya ya ce wadanda suka samu haron sun hada da matasa da 'yansanda da wasu masu sa kayan sarki. Ya ce horon ya hada da taimakamasu su kawar da tsoro idan an kawo masu hari lamarin dake faruwa da can. Ya yi amanna cewa horon zai taimakesu kuma zai shawo kan aukuwar ta'adanci. Ya ce kafin wani ya san abun dake faruwa su matasan zasu riga su gansu. An koya masu cewa idan sun ga masu shirin shirya ta'adanci su kai rahoto wurin 'yansanda ko wasu mahukunta. Su ne zasu san abun da zasu yi. Horan bai hada da yin anfani da makami ba. Nasu kawai idan sun gani su mika da rahoto gaba.
Shi ma jagoran masu bada horon daga cibiyar tsaro ta kasa da kasa dake kasar Isra'ila Mizra David ya ce cibiyar tasu ta horas da mutane fiye da dubu goma sha shida daga kasashe daban daban na duniya, ta yadda zasu dakile ayyukan ta'adanci a kasashensu. Ya ce horaswar bata yaki ba ce ko ta fada, a'a suna horas da mutane kan dabarun da zasu iya yin anfani dasu su dakile tashin hankali da ta'adanci kamar yadda suke anfani da shi a kasar Isra'ila.
Wasu da suka samu horon sun fadi albarkacin bainsu. Wani Bitrus daga Langtang Ta Kudu ya ce sun koyi yadda zasu wayar da kawunan mutane game da zaman lafiya.
Ga cikakken rahoto daga Zainab Babaji.