Mataimakiyar Kwamishanan 'yansandan jihar Oyo Janet Agbarice ta wakilci kwamishanan 'yansandan Alhaji Abdulkadiri Mohammed Indabawa a wurin taron bitan da aka yi jiya Talata a birnin Ibadan babban birnin jihar. Makasudin bitar shi ne domin su ilmantar da yara tun suna kanana kafin su girma su soma kin jin magana dangane da laifufuka. Amma idan suna kanana duk abun da aka gaya masu zasu yadda kuma zasu amince. Kwamishanan ya kara da cewa ilmantar da kananan yara tun da wuri zai rage masu aiki can gaba ba zasu dinga gudu suna fama da yara ba. Su ma yaran zasu san cewa aikata laifuka bashi da kyau.
A nashi jawabin shugaban karamar hukumar Ibadan Ta Kudu Maso Gabas Alhaji Tajudeen Bolaji ta bakin sakataren karamar hukumar Mr. John Ige cewa ya yi a yayin da yara ke girma yakamata su yi hankali kamar yadda 'yansanda suka shaida masu. Kada su aikata lafuka domin aikata laifuka bashi da kyau.
Wasu yara 'yan makaranta sun fadi albarkacin bakinsu dangane da bitar. Wani Adegba Ibrahim ya ce an koya masu kada su yi sata kada su yi karya kuma su yiwa iyayensu biyayya. Ita kuma Shola Eniola ta ce an koya masu su yiwa iyayensu da'a kada kuma su aikata laifi.
Rundunar 'yansandan ta sanar cewa irin wannan bitar za'a yita a duk cikin kananan hukumomi talatin da uku dake cikin jihar Oyo.
Hassan Umaru Tambuwal nada rahoto.