Lafiyata Kalau, Na Shirya Tsaf Don Shugabantar Najeriya - Tinubu

Dawowar Zababban Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu Najeriya Bayan Kammala Hutu A Ketare 4

Tinubu ya bayyana haka ne a gidansa da ke unguwar Asokoro a Abuja jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Faransa.

Yayin da ya dawo Najeriya daga kasar Faransa a ranar Litinin, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce lafiyarsa kalau sabanin rade-radin cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

Tinubu ya bayyana haka ne a gidansa da ke unguwar Asokoro a Abuja jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Faransa.”

Dawowar Zababban Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu Najeriya Bayan Kammala Hutu A Ketare 3

Da yake jawabi ga magoya bayansa, ya ce cikin barkwanci, “bari na huta da daren nan bayan doguwar tafiya a jirgin sama. Na ci Amala da ewedu. Bayan haka, zan dan yi barci kadan sannan gobe za mu hadu.”

Dangane da jita-jita game da lafiyarsa, Tinubu ya ce “Duk abun da su ke so suna rade-radi. Ina da lafiya, lafiya kalau.”

Gidan talbijin na Channels da ya ruwaito labarin ya ce zababben Shugaban kasar ya ce ya shirya tsaf domin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, inda ya kara da cewa yana ci gaba da tuntubar wadanda za su kasance cikin gwamnatinsa.

Dawowar Zababban Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu Najeriya Bayan Kammala Hutu A Ketare 1

“Ba za ka yi mulki kai kadai ba; kana mulki ne tare da mutane. Ku yi shawara, ku tattara sannan ku fara aiki,” in ji shi.

Tinubu ya dawo tare da matarsa, Sanata Oluremi; yayin da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC suka tarbe su da suka hada da mataimakin zababben shugaban kasa Kashim Shettima, Gwamnan Filato Simon Lalong, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila.