A wani taron manema labarai na kasa-da-kasa da aka gudanar a babbar cibiyar 'yan jarida da ke nan Washington DC, wakilan na Tinubu sun ce kura-kuran da aka samu a zaben, basu kai nauyin da za'a soke zaben baki daya ba.
Karamin ministan kwadagon Najeriya Festus Keyamo Kenan, wanda kuma shi ne mai Magana da yawun wakilan na Bola Ahmed Tinubu, yake kokarin kawar da shakku da tababar da suka ce ana kokarin cusawa a zukatan ‘yan Najeriya da ma duniya baki daya, dangane da sahihancin zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata hukumar tsaron Najeriya ta farin kaya wato DSS, ta fitar da wata sanarwa, inda take cewa ta gano wata makarkashiya da wasu ke shiryawa, na ganin cewa ba’a rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban kasa ba a ranar 29 ga watan Mayu.
Gabanin nan kuma tuni da manyan jam’iyyun siyasar kasar suka yi watsi da sakamakon zaben, bisa zargin coge da tafka magudi ta hanyar kin saka sakamakon zabe a na’urar BVAS kamar yadda dokar zabe ta tanada, inda tuni ma wasu suka garzaya kotu.
To sai dai a tattaunawar mu da daya daga cikin wakilan na Tinubu a wajen taron, kuma ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya ce kura-kuran da aka samu ba su kai nauyin soke zaben baki daya ba kamar yadda wasu suka nema.
Daya daga cikin Abubuwan muhawara a zaben na Tinubu dai shi ne rashin lashe zabe a babban birnin tarayyar kasar, wanda wasu ke ganin yana cikin sharudan ayyana nasarar dan takara, kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayyana.
To sai dai Sunday Dare na ganin matsala ce kawai ta fassara, amma manufar a fili take.
Sashe na 134 na kundin tsarin mulkin Najeriya yayi tanadin cewa, kari kan wasu sharuda, sai dan takara ya lashe kashi 25 na kuri’u daga akalla kashi 2 bisa 3 na jihohin kasar da babban birnin tarayya, kafin a ayyana shi a zaman zababben shugaban kasa, lamarin da ya haifar da sabanin fahimta a tsakanin ‘yan siyasa, har ma da wasu masana shari’a a kasar.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna daga Washington DC: