WASHINGTON, D.C. - Okonjo-Iweala, mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da ta jagoranci Cibiyar Kasuwanci ta Duniya-WTO, an saka su a cikin wannan jerin tare da Shugaban Amurka Joe Biden, Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka Kamala Harris; Xi Jinping, shugaban kasar China, da Narendra Modi, Firai Ministan Indiya, a jerin mutane mafiya tasiri da mujallar ta wallafa na 2021.
Jerin mutane 100 mafiya tasiri a duniya da Mujallar Times ta ke fitarwa shekara-shekara, yana fifita mutanen da suka taka rawar gani a “canza duniya, ba tare da la'akari da abinda ya biyo bayan abinda su ka yi ba".
Da take rubutu game da Tinubu, Mujallar ta bayyana cewa, “Cin zabe a kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka ba abu ne mai sauki ba. Sai dai zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kwashe kusan shekaru ashirin yana shiryawa. Magoya bayansa da ake kira “Jagaban”, ko kuma “shugaban Jarumai,” wanda yanzu dan shekaru 71 a duniya ya tsaya takara a zaben shugaban kasa a karon farko a wannan Maris.
Taken yakin neman zabensa, “Lokaci na ke nan,” ya nuna gamsuwa da rawar da ya taka a matsayinsa na wanda ya dade yana tsayawa da kuma shigewa ‘yan siyasa gaba da neman masu goyon baya. Tinubu ya taimaka wajen dawo da dimokuradiyyar Najeriya a shekarar 1999 bayan yakar mulkin soja sannan ya yi wa'adi biyu a jere a matsayin gwamnan Legas.