Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Na’am da Kafa Rundunar G5 Sahel

Sojojin kasar Mali suna atisaye

Kwamitin tsaro na majlaisar dinkin duniya ya yi na’am da shawarar da kasashen yankin SAHEL suka gabatar ta hanyar kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika- AU, domin kafa rundunar hadin guiwar G5 Sahel mai alhakin yakar ‘yan ta’adda akan iyakokin kasar Mali da makwaftanta.

Taron kwamitin tsaron da aka gudanar a birnin Nyame ne ya sanar da yin na’am da yunkurin da kasashe biyar na yankin Sahel suka sa gabatar domin murkushe kungiyoyin ta’addancin dake addabar kasar Mali da makwabta, ta hanyar kafa rundunar hadin guiwa ta G5 Sahel.

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamhuriyar Nijar Alhaji Ibrahim Yakuba ya bayyana cewa, wannan zai kara karfin guiwa ga kasashen da kuma dukan wadanda suke son su taimaka masu domin ganin sun cimma nasara.

Ministan yace idan aka tara sojojin kimanin dubu biyar aka kuma dauki lokaci ana iya cimma nasara. Ya bayyana cewa, suna so su sami irin nasarar da aka cimma a Najeriya wajen karya lagon kungiyar, inda suke hankoron ganin sun hana ‘yan ta’adda kai hare hare a cikin Mali balle har su fita wadansu kasashen ketare.

Sai dai sharuddan da kwamitin tsaron na majalisar Dinkin Duniya ke aiki a karkashinsu suka gindaya, sun kawo cikas wajen ba kasashen na Burkina Faso, Mali, Nijar, Chadi da Mauritaniya cikakken goyon bayan da zai basu damar kai farmaki har can gindin magani.

Alhaji Ibrahim Yakuba ya bayyana cewa, sun so a basu damar su iya shiga har Mali ko kuma su isa kan iyaka da kasar su kai hari a cikin wani izini dake karkashin tsarin.

Ya bayyana cewa Kungiyar kasashen Tarayyar Turai ta ba rundunar hadin guiwar tallafin kimanin saifa miliyan talatin kwanakin baya, suna kuma neman sauran kasashen su bada nasu tallafi kasancewa matsala ce da ta shafi dukan kasashe .

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya aiko daga birnin Nyame.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Tsaro ya yi na'am da kafa rundunar tsaro ta Sahel-2'55