Bisa la’akari da ci gaba da fadadar kungiyar a Libya, da kuma mummunan harin nan da aka kaiwa birnin Faris ta kasar Faransa a watan Nuwambar bara, wannan ta sa jami’an na Amurka ke ganin akwai bukatar fadada kawancen soji ta nan bangaren.
Wani babban jami’in diflomasiyya da ya nemi a sakaya sunansa ya fadawa Muryar Amurka cewa, “tabbas an tattauna wannan maganar, sannan kuma ana ma ci gaba da yin maganar bisa yadda ya kamata aa bullowa lamarin”.
Wannan maganar na bukatar a karkareta cikin gaggawa idan aka yi la’akari da yadda mayakan ISIS ke dada kutsawa cikin Libya daga kan iyakokin Afirka ta Arewa, ta gabashi da kuma ta yankin Sahel.