Ministocin ayyukan noma da kiwo da kwamishanonin kungiyar kasashen yammacin Afirka masu anfani da sefa suka taru a Nijar domin nazarin hanyoyin da zasu samu mafita daga lamarin da ya shafi kasashen su takwas, wato karancin abincin mutane da na dabbobi.
Alkalumma sun nuna cewa mutane 257,000 ne ke fama da yunwa a Bukina Faso. Mali nada mutane 601,000 dake cikin yunwa. Senegal tana da 425,000. Guinea Bissau nada 33,000 dake fama da yunwa. Kasar Togo nada 21,800.A jamhuriyar Benin an gano mutane 18,000. Amma kasar Nijar ce tafi kowace kasa fama da matsalar cimaka inda aka kiyasta mutane 1, 313,000 ne ke bukatar agajin gaggawa.
Matsalar Nijar nada nasaba da 'yan gudun hijiran Mali da Najeriya, kasashe biyu dake fama da ayyukan 'yan ta'adda.
An bukaci kasashen su yi wani abu kafin isowar agaji daga kasashe masu hannu da shuni, inji ministan bunkasa ayyukan noma da kiwo na kasar Nijar Albade Abuba.
Wani kalubalen da kasashen suka ce yana fuskantarsu kuma shi ne abun da ya shafi kiwo wanda shi ma yana fuskantar karancin cimakar dabbobi. Akwai kuma bullar cututtuka dake yiwa dabbobi da kiwon barazana. Haka kuma mutuwar kifaye na kara ta'azzara.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum