Jami'an sojin Faransa da kuma shaidu sun ce an kai harin ne ta sama da ta kasa a wani kurmin da ke yankin na Sahel.
Sojojin Faransa wajen 3,500 ne ke baje a fadin kasar ta Mali da Burkina Faso da da Chadi da Mauritania da Nijar su na fafatawa da masu tsattsauran ra'ayin addini.
Mali ta tsawaita dokar ta bacin da ta kafa da karin wasu watannin 6, a yayin da ta ke kokarin taka burki na wata kungiyar 'yan tawaye mai alaka da al-Qaida da ke arewacin kasar, da kuma wasu masu tsattsauran ra'ayin wadanda ke kaddamar da hare-hare daga Burkina Faso.
Facebook Forum