Kwamishanan 'Yansandan Jihar Borno Ya Musanta Rahoton Sace Wasu Mata

Matan Fulani.

Yayin da kafofin labaru na Najeriya da na waje suke cewa wasu 'yan bindiga sun sace wasu matan Fulani a wata rugarsu dake kusa da Chibok, kwamishanan ;yansandan jihar Borno ya musanta rahoton
Duk da musanta rahoton sace wasu matan Fulani daga rugarsu dake kusa da garin Chibok da kwamishanan 'yansandan jihar Borno yayi, kafofin labaru na cigaba da tabbatar da aukuwar lamarin.

Rundunar 'yansandan dai ta jihar Borno ta karyata rahoton dake cewa an sace wasu matan Fulani kusa da garin Chibok a kudancin jihar. Kwamishanan 'yansandan Lawal Tanko shi ya shaidawa wakilin Muryar Amurka hakan a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Kwamishanan yace bashi da wani rahoto game da sace matan Fulanin.Yace ya tuntubi jami'insa dake garin Chibok game da rahoton shi ma yace bashi da masaniya. Kwamishanan yace shi ma daga bakin 'yan jarida yake jin labarin sabili da haka ba zai iya cewa komi ba.

Shi ma shugaban karamar hukumar Chibok Mr. Ban Lawan yace kawo yanzu bai samu wani rahoto akan batun ba. Shi ma kamar kwamishanan 'yansandan ya ji ne ta kafofin labarai.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamishanan 'Yansandan Jihar Borno Ya Musanta Rahoton Sace Wasu Mata - 1'37"