Kwamandojin Boko Haram Sun Bindige Jagoransu Mamman Nur

Rahotanni masu tushe dake fitowa daga zirin tafkin Chadi na nuna cewa kwamandojin mayakan boko haram sun bindige jagoransu, Mallam Mamman Nur dake wa Abubukar Al-Bagadaji mubaya’a.

A shekarar 2014 ya jagoranci wasu mayakan suka balle daga uwar kungiyar Boko Haram da Abubakar Shekau ke jagoranta inda Abu Albarnawi ya zama amir din su, baya ga kafa sansannin su a zirin tafkin Chadi dake arewacin jihar Borno.

Mamman Nur, wanda ya haddace Al’Qurani tare da kwarewa a harshen labarci da mu'ammala tsakanin mabiyansa, wanda yayi silar kulla alaka tsakanin kungiyar ta’addar ISIS a bangarorin Boko Haram a kasashen yankin tafkin Chadi.

Kwamandojin Boko Haram mabiyan Mamman Nur, sun kashe shi ne bisa zargin cewar ya cika sassauci da daukan lamura sannu a hankali. Majiyoyi sun tabbatar da cewa ko sako 'yan matan Dapci da suka yi garkuwa da su da aka yi a baya bayan nan shima ya kara hura wutar rikici a tsakanin su.

Immam Abubukar bin Abdullah, da suka yi yunkurin jagorantar shiga tsakanin Boko Haram da Gwamnati ya ce makomar Boko haram yanzu haka ba ta da kyau, kuma aukuwar wannan lamari alheri ne ga gwamnatin tarraya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamandojin Boko Haram Sun Bindige Jagoransu Mamman Nur 2'59