Rashin hukunta wadanda suka aikata laifuka ko nuna son rai a sha’anin shari’a na daga cikin manyan dalilan da masana suka aiyana a matsayin wadanda suka jefa kasashen yammacin Afirka da na SAHEL cikin yanayin tashin hankali.
Dalili kenan da MDD da kungiyar AU da Ecowas ko CEDEAO suka tattara masana domin nazarin wannan matsala da a karshe illolinta ke karewa akan talakkawa. A saboda haka wakilin sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD a wannan yanki Dr IBN CHAMBAS ya ja hankulan shuwagabanni.
Yana mai cewa dole ne a dauki matakan mutunta ‘yancin dan adam kamar yadda ya zama wajibi a shimfidar da shari’ar adalci da gaskiya domin kawo karshen tashin tsahina bisa la’akari da cewa mafi yawancin rigingimu kan samo tushe ne daga dabi’ar fatali da doka.
Dr. Chambas yace wannan ya sa a yayin wannan taro muka ja hankula gwamnatoci akan bukatar daukar matakan inganta fannin shara’a a kowane mataki har zuwa yankunan karkara domin ba al’ummomi damar morar yancinsu.
Gwamatocin kasashen da suka halarci wannan taro a ta bakin ministan shara’ar Niger MAROU AMADOU sun bukaci MDD ta sake gudanar da irin wannan taro. Ya kasance cikin jerin mahimman aiyyukan da ke kunshe cikin ajandarta don ganin kasashen yankin Sahel da na Afirka ta yamma sun hadu a wuri daya lokaci zuwa lokaci da nufin bitar hadin gwuiwa a game da tafiyar da harakokin shara’a a daukacin wadanan kasashe dake fama da kalubalai iri guda wato ta’addanci, safarar makamai, fataucin miyagun kwayoyi har da dai sauransu.
Dr IBN CHAMBAS ya kara da cewa cimma burin da aka sa gaba a karkashin irin wannan haduwa ya danganta da yanayin rayuwar ma’aikata da na kayan aiki a mashara’antu. Ciki kuwa har da maganar bayarda albashi mai tsoka ga alkalan shara’a da mataimakansu yayinda a daya gefen ya zama wajibi a tanadi wadatatun kayan aiki.
Wannan shawara na zuwa ne a wani lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin kungiyar alakalai da hukumomin shara’a a Niger akan zargin hukumomi da rashin mutunta hukuncin kotu.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum