Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Bangar Siyasa A Adamawa


Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibirila
Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibirila

Yayin da ake haramar zaben tsayar da yan takara a jam’iyun siyasar Najeriya, wata matsalar dake barazana ga zaben dake tafen itace ta yan bangan siyasa,da ke neman gagaran kundila a jihar Adamawa.

Wasu yan bangar siyasa sun yi cincirundo sun baza hajarsu a sakatariyar wata jam’iyya a jihar Adamawa, batun da yanzu ke zama barazana a harkokin siyasa.

Koda yake su wadannan yan jagaliyar ba ruwansu da jam’iyya, lamarin ya fi kamari ne a manyan jam’iyyu,musamman jam’iyyar dake mulki, jam’iyar APC inda wasu kusoshin jam’iyar suka sha da kyar a hannun yan jagaliyar.

Ahmad Lawal shine sakataren tsare tsare na jam’iyyar a Adamawa,yace su kullum suna kwaban magoya bayansu, to amma duk da haka wasu matasa sun farmasu.

Tuni aka soma nuna yatsa game da wannan matsala ta yan bangan siyasan inda wasu ke zargin bangaren gwamnan jihar Bindow Jibrilla da daukan nauyin yan jagaliya,zargin da kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo ya musanta.

DSP Habibu Musa, mukaddashin kakakin rundunan yan sandan jihar ya ce tuni suka daura damara.

A Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG