A taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin kwadagon na cibiyoyin bincike ta kira, sun bayyana cewa shekaru da dama gwamnatin tarayya ta ke rikon sakainar kashi saboda rashin bada isasshen kudade don inganta ayyukan bincike a cibiyoyin dake samar da duk wani abinda al’umma ke amfani da shi, tun daga kan magunguna, ma’adinai, karafa, ayyukan gona, muhalli, cimaka da sauransu.
Komared Luka Malaya Maigari ya ce sau talatin da uku sukayi zaman tattaunawa da gwamantin tarayya amma har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba, don haka suka shiga yajin aiki.
Komared Umar Dan Halilu ya ce sun fito ne su yi wa gwamnatin tarayya tuni kan alkawuran da tayi.
Shugaban hukumar binciken harkokin noma ta tarayya, Farfesa Garba Hamidu Sharubutu ya ce gwamnati na daukar matakan warware matsalar.
Saurari cikakken rahoton a cikin:
Your browser doesn’t support HTML5