Kungiyoyin Kasashen G5 Sahel Sun Hada Gwiwa Don Shawo Kan Matasa

Taron Yan Majalisun Dokoki G5 Sahel A Kasar Niger.

Tawagogin matasa daga kasashen G5 Sahel sun hallara a jamhuriyar Nijar don tattauna hanyoyin kafa wata majalisar matasan kasashen wannan yanki a ci gaba da neman hanyoyin kare matasa daga tarkon ‘yan ta’adda a wannan lokaci na yawaitar aika-aikar ‘yan bindiga.

Lura da yadda kungiyoyin ta’addanci ke amfani da matasa wajen tafka ta’asar dake wakana a yanzu haka a yankin Sahel ya sa kungiyar majalisun dokokin kasashen Afirka rainon Faransa wato APF da kungiyar kasashen G5 Sahel fara yunkurin kafa wata majalisar matasan kasashen G5 wacce za a dora wa nauyin waye kan matasan yankin ta yadda zasu kauce wa fadawa hannun kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan fashi, mafarin wannan taro kenan a cewar mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijar Hon. Kalla Hankourao.

Mutane kimanin million 83 ne aka kiyasta cewa suna zaune a yankin Sahel kuma kashi 60 daga cikin 100 na yawan wadanan al’ummomi matasa ne saboda haka ya zama wajibi a fara ayyukan ganar da matasa irin rawar da ya kamata su taka a kokarin fitar da wannan yanki daga matsalolin tsaro da na tattalin arzikin da ya tsunduma ciki inji Dah Sansan Tilkouete, dan majalisar dokoki mai wakiltar kasar Cote d’ivoire a majalisar APF.

Matashiya daga jihar Damagaram, Yasmina Aboubacar Yacouba Siddo dake daya daga cikin mahalartan wannan taro, tana da kwarin gwiwar cimma burin da aka sa gaba a karkashin wannan majalisa ta matasa da ake shirin kafawa.

Mayar da hankali akan batun ilimi da tarbiyya ita ce hanya mafi a’ala a yau wajen kare matasa daga yunkurin kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan bindigar da suka addabi kasashen Sahel, sakon da Salma Hala wata matsahiyar kasar Mauritaniya tace ta zo da shi kenan da sunan matasan Mauritaniya zuwa ga matasan kasashen nan 5 wato Nijar, Mali, Burkina Faso, Chad da Mauritania.

Rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kasashen G5 Sahel Sun Hada Gwiwa Don Shawo Kan Matasa