Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiran Da A Binciki Tsohon Shugaba Mahamadou Issouhou Na Nijar


Shugaba Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijer wasu kungiyoyin fafitika sun bukaci gwamnati kasar ta gurfanar da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issouhou a gaban shara’a sakamakon zarginsa da tafka mumunar barna a zamanin da yake kan karagar mulki; sai dai wasu makusantansa na cewa wannan yunkuri ne na neman raba kan ‘yan jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki.

A sanarwar da su ka fitar a yau jumma’a shugabannin kungiyar Tournons la Page sun fara ne da zayyana jerin almudahanar da su ka ce an tafka a zamanin tsohon shugaban kasar Nijer, Mahamadou Issouhou. Su na masu zarginsa da alhakin dukkan abubuwan da suka kira ayyukan asha da aka tafka a wancan lokaci. Saboda haka suka bukaci a gurfanar da shi a gaban koliya kamar yadda shugaban reshen kungiyar na yankin Yamai Moudi Moussa ke Karin bayani.

Kungiyar ta Tournons la Page ta ce kafa rundunonin sojojin kasashen waje a nan Nijer da sunan yaki da ta’addanci wani abu ne da ya samo tushe a lokacin da Mahamadou Issouhou ke rike da madafun iko . Rashin samun bayyanannen sakamako a wannan yaki ya sa kungiyar nuna bukatar ficewar wadannan dakaru da ta kira sojojin mamaya, duk kuwa da cewa mahukunta sun sha nanata cewa aikin horon jami’an tsaro da samar da bayanan sirri ne ke tafe da su. Ismael Haldi shi ne mataimakin shugaban Tournons la Page na kasa baki daya.

Da yake maida martani akan wadannan bukatu na ‘yan farar hula, wani na hannun daman tsohon shugaban kasar Nijer, wato Assoumana Mahamadou na kallon abin a matsayin wata makarkashiyar siyasar da aka kitsa da nufin ratsa jam’iyya mai mulki.

Baya ga maganar tabarbarewar sha’anin tsaro, kungiyar ta Tournons la Page, a wannan sanarwa, ta nuna damuwa a game da koma bayan sha’anin ilimi, inda rashin tanadin ingantattun dakunan karatu ya yi sanadin mutuwar yara 20 a bara a Yamai yayin da wasu sama da 20 suka kone kurmus a farkon watan nan na Nuwamba a Maradi, bayan da gobara ta rutsa da su a azuzuwan karatu na zana.

Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG