A yau aka kammala wani taron manoma da makiyaya a Jamhuriyar Nijar, wanda aka yi a jihar Dosso, inda suka mika koken su ga shugaba Mohamed Bazoum, da kuma jerin matsalolin da ke tauye ayyukan noma da kiwo a kasar da galibin jama’arta ke rayuwa a karkara, shugaban kuwa ya sha alwashin daukar matakan shafe hawayen jama’a a wannan fanni.
A jawabin da ya yi wa mahalarta taro da hantsin yau Alhamis, a kauyen Margou da ke gundumar birnin Gaore, shugaban kasar ya fara da jinjina wa shugabanin kungiyoyin ci gaban karkara, saboda mahimmancin irin wannan haduwa ta neman mafitar matsalolin da suka addabi Nijar, shekaru aru aru a fannin samar da cimaka.
Bayanan hukumomin Nijar, sun yi nuni da cewa, gardamar da aka fuskanta a damanar da ta gabata ta haddasa babban gibi, idan aka kwatanta da amfanin da aka saba girba a shekarun baya, saboda haka Mohamed Bazoum, ya bayyana shirin aiwatar da wani fasali don tallafa wa mutane sama da million 8 dake cikin halin bukata.
Shugabannin kungiyoyin ci gaban karkara irinsu Saley Souley, na kungiyar AREN sun yaba da wannan yunkuri, to amma kuma mafi a’ala shi ne gaggauta soma zartar da wannan tsari, domin tun a yanzu talakawa na cikin halin matsi.
Mahimmancin wannan batu na tunkarar halin karancin abincin da ake ciki a bana, sanadiyyar gardama ya sa Firai Ministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou, kiran taron jakadun kasashen waje da na kungiyoyin kasa da kasa, a farkon makon nan domin neman gudunmowarsu akan wannan al’amari a cewar shi.
Za a iya sauraron cikakken rahoton Souley Moumouni Barma, a cikin sauti.