Bisa ga wasikar da mahukumtan birnin Yamai suka rubutawa kawancen kungiyoyin ya sa suka dage taron gangamin da suka shirya yi jiya Lahadi a brnin.
Tuni kungiyoyin suka shirya bullo da wani salon na daban. Musa Sangari daya daga cikin jagororin kungiyoyin yace hanasu yin zanga zanga nuni ne cewa suna da gaskiya bisa ga zargin da suke yiwa gwamnatin na son kafa mulkin kama karya. Yace dole zasu fito su yi gwagwarmaya domin idan basu yi ba gwamnati mai ci yanzu zata jefa kasar cikin mulkin kama karya.
Shugabannin sun kira duk mutanensu su zauna gidajensu ranar Alhamis Afirilu 28, 2016. Dangane da zanga zangar da suka shirya suka ce zasu yi ranar Asabar mai zuwa, wato Afirilu 30, 2016.
A zantawa da ya yi da Muryar Amurka shugaban hadin kungiyoyin dake goyon bayan gwamnatin shugaba Mahammadou Issoufou, Abdu Mamman Lukoko ya bayyana cewa dimokradiyar Nijar na nan daram. Yace dimokradiya ce ta sa a ka bar kungiyoyin adawa suna fadin abubuwan da suke fadi. Yace wani wuri ko mutum na son fadin magana ba zai yi ba domin ya san inda za'a ajiyeshi. Yadda 'yan adawan suka shiga kafofin labarai suna bayyana ra'ayoyinsu abu ne da dokar kasa ta tanada. Taba kowa 'yancin ya fadi albarkacin bakinsa a karkashin mulkin dimokradiya.
Lukoko yace su ba zasu shiga zanga zangar ba domin bujirewa doka ne. Ba zasu goyi bayan karya dokar kasa ba. Idan ana karya doka to babu dimokradiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5