NAIMEY, NIGER - Hakan zai tabbatar da dimokradiya a tafiyar irin wadanan kungiyoyi da ke da alhakin dora ‘yan siyasar nahiyar Afrika a kan hanya musamman akan maganar mutunta wa’adin mulkin kasa.
Shugabancin kungiyar farar hula a Nijar wani abu ne da a wasu kungiyoyin aka mayar da shi tamkar mutu ka raba takalmin kaza duk kuwa da cewa irin wannan tafiya abu ne na jama’a da ya kamata a bai wa kowane mamba damar ya ja ragama ta hanyar zabe.
Dalilin da kenan kungiyoyin sama da 30 mambobin gamayyar Tournons La Page a karshen taronsu na shekara shekara suka shawarci sauran takwarorinsu, su fara aiki da tsarin kayyade wa’adin shugabanci, Wanda a a ganin su yin haka alama ce ta nuna kishin dimkoradiya.
A kasashen dimokrdiya doka ta dora wa kungiyoyin fararen hula alhakin zuba ido akan tafiyar sha’anin mulkin kasa domin tabattar wa kansu cewa ba a kauce wa ka’ida ba saboda haka shugaban kungiyar kare hakkin jama’a ta La Voix Des Sans Voix Nassirou Saidou ya yaba da wannan shawara ta Tournons la Page.
A cewar shugaban kungiyar Mojen Siradji Issa ba yau ba su ke fatan ganin an shimfida tsarin kayyade wa’adin shugabancin kungiyoyi ta yadda hukumomi za su sami cikakkiyar masaniya a game da irin waynar da jam’an fafitika ke toyawa.
A nan gaba kungiyoyin na Tournons La page za su gudanar da zagaye domin wayar da kan jami’an fafitika akan wannan batu na shigar da tsarin kayyade wa’adin shugabanci a dokokin gudanarwar kungiyoyi masu zaman kansu matakin da ba’idin kasancewarsa hanyar tabbatar da dimokradiyar kungiyoyi a dai gefe yunkuri ne na shirya matasan da za su gaji shugabanin da ke cin yanzu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5