NIAMEY, NIGER - Kwayoyin tramadol samfarin Royal kimanin 339,364 da kwayoyin EXOL da ake kira farin malan kimanin 8,000 ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato OCRTIS ta gabatar wa manema labarai wadanda ta ce jami’anta sun kama a hannun wasu mutane 5 dukkansu ‘yan Nijar bayan gudanar da binciken da ya kai su kauyen Yaboni da ke kewayen birnin Yamai.
Hukumar ta kuma gabatar da motoci 3 da babura 2 hade da zunzurutun kudi miliyan 5 da ‘yan kai na CFA da wasu kayayyaki na daban wadanda tace ta kama a hannun wadannan masu safara.
Mataimakin alkali mai kare muradan gwamnati a babbar kotun birnin Yamai substitu du Procureur Boubacar Amadou Souleymane, ya yaba da wannan aiki da ke bukatar samun goyon bayan al’umma da gwamnatin Nijar.
Duk da matakan da hukumomi ke dauka don kara zuba ido akan hanyoyin zirga-zirga, fataucin miyagun kwayoyi wani al’amari ne da ke kara tsananta a ‘yan shekarun nan a Nijar, abinda ke nunin bukatar kara maida hankali wajen ayyukan fadakarwa, a cewar Idrissa Amadou sakataren kungiyar LCDJ kariyar matasa.
Safarar miyagun kwayoyi wani babban laifi ne da dokokin Nijar suka tanadi hukunci akan dukkan wanda aka kama da hannu a ciki, inda a kan iya kulle mutun a kurkuku daga wata 1 zuwa shekara 1 ko shekaru 10, har zuwa shekaru 30, bisa ga girman laifin da mutun ya aikata.
Saurari rahoton cikin sauti: