NIAMEY, NIGER - Tuni dai saukar ruwan saman mai yawan gaske ya janyo ambaliyar ruwa da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 20, da kuma asarar dimbin dukiyoyi.
Tun a jajibirin shiga daminar bana ma’aikatar hasashen yanayi ta bada sanarwar hango yiwuwar tafka ruwan sama fiye da shekarun baya bisa la’akari da girman tasirin illolin canjin yanayi a Nijar, abinda ka iya haddasa ambaliya a wurare da dama kamar yadda bayanai ke nunawa.
Ruwan da aka tafka daga tsakiyar watan nan na Yuli kawo yanzu ya janyo hasarar rayukan mutane, da dabbobi, da kuma dukiyoyi.
Jihar Damagaram ce aka bayyana a matsayin mafi fuskantar wannan bala’i inda mutane sama da 200 suka fake a wuni guda kawai a kauyen Hamdara.
A taron manema labaran da ya kira shugaban ma’aikatar agajin gaggawa ta Direction Generale de la Protection Civile, mamba a kwamitin hadin guiwa na COVACC Colonel Boubacar Bako ne ya yi karin haske a kan halin da ake ciki.
Wannan ya sa kwamitin COVACC soma jan hankalin al’umma da yin taka-tsan-tsan a matsayin riga kafi.
Ambaliyar ruwa wani al’amari ne da ke tsananta a kowace shekara a Jamhuriyar Nijar kasancewarta daya daga cikin kasashen Sahel, yankin da masana suka ayyana a matsayin mafi fama da matsalolin canjin yanayi a duniya, kamar kwararowar hamada da zaizayar kasa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: