Lura da yadda jama’a ke ci gaba da kokawa akan yanayin tsadar rayuwar da ake ciki a Nijer tun bayan kaddamar da dokar harajin 2018, ya sa wadanan kungiyoyin fararen hula a karksahin jagoracin Nouhou Arzika da Ali Idrissa da Moussa Tchangari, kiran daukacin ‘yan Niger su fito kan tituna a ranar 9 ga watan gobe a ci gaba da nuna adawa da wannan dokar haraji kamar yadda sanarwar da suka fitar ta fada.
Watanni sama da 8 kenan da hukumomin suka fara zartar da sabuwar dokar harajin da ake takaddama a kanta saboda haka Alhaji Usumana Mahamdu wani na kusa a jam’iyar PNDS mai mulkin kasar, ke ganin masu fafutika sun makara. A cewarsa 'ya Niger yanzu sun gane cewa masu fafutikan ba domin talakawa suke yi ba, su na da wata manufar siyasa.
Rufe ido akan dokar harajin 2018 tamkar sakarwa mahukuntar ragama ne su cusa wasu matakai na daban a daftarin dokar harajin shekara mai zuwa abin da ka iya kara jefa talakkawa cikin kuncin rayuwa inji Nouhou Arzika.
Tun a karshen shekarar 2017 ne kungiyoyin fafutika suka kaddamar da gwagwarmaya domin tilastawa gwamnatin kasar ta canza ra’ayi akan wasu sabbin matakan da ke kunshe a dokar harajin 2018. Sai dai kawo yanzu haka ba ta cimma ruwa ba, hasalima jagororin wannan tafiya sun tsinci kansu a gidan yari saboda zargin tada zaune tsaye, kafin a karshen watan jiya kotun Yamai ta sakesu.
A saurari rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5