Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Niger An Fara Shari’ar Wadanda Ake Zarga Da Ayyukan Ta’addanci


Zaman kotun Niger
Zaman kotun Niger

An fara shari’ar mutanen da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci a Daiffa, yankin da ya yi fama da rikicin Boko Haram a kasar Niger

Kimanin mutane 40 ne ake zarginsu da aikata ayyukan ta’addanci ko kuma hada baki da masu tada kayar baya.

A karon farko an dage shari’ar daga birnin Yamai zuwa Diffa inda rikicin Boko Haram ya yi kamari domin ragewa dangin wadanda ta’addancin ya shafa wahalar yin bulaguro zuwa Yamai domin su saurari karar.

A wannan karon alkalai uku ne zasu saurari kararraki har guda 20 yayinda aka tanadi lauyoyin da zasu kare wadanda ake tuhuma.

Mai shigar da kara a madadin gwamnatin Niger Sha’aibu Salma ya ce za’a yi shari’ar akan adalci da gaskiya. Za’a yi shari’ar a bayanai

‘Yan uwa da dangin wadanda suka fada hannu mahukumta sanadiyar zargin cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun goyi bayan zaman dari bisa dari saboda akwai masu laifi akwai kuma wadan da basu da laifi. Suna da karfin gwuiwar cewa duk wadanda basu da laifi za’a sake su.

A saurari karin bayani a rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG