'Yan fafutika kusan su 20 ne aka gurfanar dasu a gaban alkali, a shari'ar da ake yi masu wadda take cike da cecekuce.
Maganar ta samo asali ne daga gangamin da fararen hula suka yi a watan Maris na bana, suna adawa da sabbin dokokin haraji da gwamnatin ta yi cikin kasafin kudin wannan shekarar.
Shari'ar da ta kwashe sa'o'i da dama ranar Litinin, lauyoyin gwamnati da lauyoyi dake kare mutanen da ake tuhuma, sun tafka muhawara zazzafa.
Rahamanu Usman, daya daga cikin lauyoyin dake kare 'yan gwagwarmayar, ya yiwa Sashen Hausa karin bayani ta waya. Yana cewa abun da suka fahimta shi ne gwamnati ta dauki matakin ne domin ta hana mutane adawa da dokar kasafin kudi. Kowa ya san dokar ta kunshi abubuwa da dama da suka tauye hakkin talakawa, injishi.
Amma a nashi bangaren, alkali mai shigar da kara ya bukaci kotu ta yankewa wadanda ake tuhuma hukumcin zaman kaso na shekaru uku uku, wasu kuma shekara guda guda ko wata shida shida. Amma lauyoyin dake kare su sun shure bukatar, domin a cewarsu zargin da ake yiwa mutanen su bashi da tushe a dokance.
Alkali mai shari'a ya dage yanke hukumci sai ranar 24 ta wannan watan.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum