Yawan koke koken jama’a masu cinikayyar gidaje da filaye sun sa gwamnatin Jamhuriyar Niger yanke shawarar rage harajin da ta sa cikin kasafin kudin kasar na bana.
Gwamnati ta aikawa majalisar dokokin kasar da ta yiwa kundun kasafin gyaran fuska. Kakakin ‘yan adawa a majalisar Issoufou Isiyaka yace dama sun san za’a yi haka.
Yace tun farko sun fada cewa harajin da aka sa akan gidan da aka sayar ko fili ya yi yawa. Yanzu gwamnati ta gani ta komo baya. Yawan haraji ba zai sa a samu kudi sosai ba.
A wani bangaren kuma gwamnatin kasar ta umurci ma’aikatar kwastan ta kasar ta gaggauta soma aiwatar da wani tsarin harajin awon kaya matakin da tuni aka fara zullumi a kansa.
Kakakin masu adawa a majalisar dokokin kasar y ace harajin da aka sa a kan abincin da mutane da yawa ke anfani dashi kamar madara, hatsi da shinkafa kamata ya yi gwamnati ta sake dubawa ta rage harajin. Idan bata rage harajin ba zata jawowa talakawa babbar matsalar kuncin rayuwa.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum