Rashin gamsuwa da yanayin tafiyar da al’amuran mulki ya sa wasu ‘yan Nijer daukar makamai a shekarar 2019 a karkashin kungiyar ‘yan tawayen UFPR da ke da hedkwata a iyakar kasar da Libya.
Sai dai a cewarsu, lura da yadda aka fara ganin alamomin kamanta gaskiya ya sa suka amince su ajiye makamai.
Shugaban kungiyar ‘yan tawayen ta UFPR Mamhoud Salah ya bayyana dalilan da suka sa shi da wasu abokansa suka kafa kungiyar da zummar gwagwarmayar samar da mulki nagari a kasar ta Nijar.
Ya ce tun daga wancan lokaci wasu suka kaddamar da ayukan tuntubar bangarori domin shiga tsakani , ya kara da cewa "a tsawon shekaru a kalla 3 abubuwa da dama sun faru, yau mun yanke shawarar mu dawo gida mun zo mu yi sulhu da gwamnati."
"Mun yi niyyar samar da zaman lafiya a Nijar, kungiyar UFPR mun lura da sauyin da aka fara samu wajen tafiyar da lamuran kasa. Shugaban kasa ya yi mana tayin zaman lafiya saboda haka mun yi nazari mun kuma tuntubi abokan tafiyarmu muka amince mu sasanta da kasa ba tare da tsoma bakin kowane dan kasar waje ba" in ji Salah.
Kakakin kungiyar ta UFPR Abdoulkader Mahamadou Sangare ya ayyana cewa babu sharudan da suka gindaya wa hukumomi kafin su yarda su ajiye makamai, sakamakon yadda suka fahimci mahimmancin zaman lafiya suna masu yin nadamar bijirewa kasa a baya.
Shugaban jam’iyar hamayya SDR SADUWA Habibou Kane Kadaure ya yaba da wannan yunkuri na neman zaman lafiya, ko da yake a ra’ayinsa, hanyoyin da aka bi wajen kulla wannan yarjejeniya na bukatar gyara.
Daga wani yankin dake kan iyakar Nijar da Libya da kungiyar tawayen ta Union des Forces Patriotiques pour la Refondation de la Republique ta mayar da shi hedkwarta a tsawon shekarun nan 3 na baya, ta sha yada fayafan bidiyo da na murya domin tunatar da hukumomin Nijer akan manufofin da ta sa gaba.
Haka kuma kungiyar ta dauki alhakin harin da aka kai wa wani ayarin dakarun Nijer a wajen Dirkou a 2021 lamarin da ya yi sanadin mutuwar jandarma 1 tare da raunata wasu.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5