Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Tura Dakarun Soji Don Yaki Da Yan Aware


General Nka Valere, commander of Cameroon troops fighting separatists in Cameroon's English speaking Northwest region, Apr. 19, 2021. (Moki Edwin Kindzeka/VOA)
General Nka Valere, commander of Cameroon troops fighting separatists in Cameroon's English speaking Northwest region, Apr. 19, 2021. (Moki Edwin Kindzeka/VOA)

Sojojin da aka tura domin dawo da doka a watan Yuni sun kashe mayaka bakwai ciki har da wasu shugabanni ‘yan aware uku.

A wannan makon kasar Kamaru ta tura karin sojoji 300 zuwa Bui, wani sashe na arewa maso yammacin kasar da sojoji suka ce ya zama matattarar ‘yan aware.

Sojojin suna gudanar da bincike gida-gida don gano makamai da lalata abubuwan fashewa da sansanonin ‘yan tawaye. Amma fararen hula na zargin bangarorin biyu da cin zarafi da take hakkin bil adama.

Sojojin Kamaru sun ce Bui, wani yanki ne da ke amfani da turancin Ingilishi da ke Yankin Arewa maso Yamma, wanda kuma ya zama cibiyar mummunarn ta’addancin ‘yan aware.

Sojoji sun lalata kimanin bama-bamai 35 a cikin makonni biyu da suka gabata.

General Valere Nka, commander of the Cameroonian troops fighting separatists in the English-speaking North-West region, Dec. 12, 2020. (Moki Edwin Kindzeka/VOA)
General Valere Nka, commander of the Cameroonian troops fighting separatists in the English-speaking North-West region, Dec. 12, 2020. (Moki Edwin Kindzeka/VOA)

Sauran bama-baman da 'yan aware suka dasa sun lalata motoci da hanyoyi, in ji sojojin kasar.

Sojojin da aka tura domin dawo da doka a watan Yuni sun kashe mayaka bakwai ciki har da wasu shugabanni ‘yan aware uku, in ji hukumomi. Sojoji hudu sun mutu yayin kwace makamai daga hannun mayakan.

Janar Valere Nka shi ne kwamandan sojojin gwamnati da ke yaki da 'yan awaren.

Ya ce an tura karin dakaru 300 a wannan makon zuwa Bui tare da aikin lalata bama-bamai da sansanonin 'yan aware.

Nka ya ce babu lokacin hutawa ga sojojinsa kasancewar kashe-kashe da kwasan ganima da 'yan tawaye ke yi, wanda har yanzu ake ta fama da shi a Bui.

Ya ce mayaka na ci gaba da yin barazana ga 'yanci da walwala ga fararen hula, yana mai cewa Shugaba Paul Biya, wanda shi ne babban kwamandan askarawan Kamaru, ya umarci sojoji da su rusa sansanonin ‘yan aware da kuma kawar da‘ yan tawaye da masu kiran kan su shugabanni.

Nka ya bukaci fararen hula da su taimakawa sojoji wajen kai rahoton duk wadanda ake zargi, da kuma taimakawa wajen gano maboyar su.

XS
SM
MD
LG