Jami'an sun ce. ‘yan tawayen na tserewa daga kasar ne don gujewa tashin hankalin da zai biyo bayan zaben.
Jami'ai a Kamaru sun zargi ‘yan tawaye da shiga yankin kasar da kuma muzgunawa fararen hula da sauran wadanda suka rasa muhallansu ta hanyar fada a makwabciyar kasar.
Jami’ai sun ce daga nan ne ‘yan tawayen suka kwace shanu da abinci daga makiyayan Kamaru da manoma. Kimanin fararen hula 30 aka sace a watan Yuni tare da neman ‘yan uwan su biya kudin fansa tsakanin $ 1,000 zuwa $ 10,000 ga kowane mutum don tabbatar da sakowar su lafiya.
Mahukunta sun ce mutanen da ake zargi da hada kai da jami’an Kamaru sun yi tir da ‘yan tawayen, wadanda ke buya a kauyukan da ke kan iyakar Kamaru, su ma an sace su tare da azabtar da su don ramuko.
Kildadi Tagueke Boukar shi ne gwamnan yankin Adamawan Kamaru wanda ke da iyaka da Afirka ta Tsakiya. Ya ziyarci Mbere, wani sashin gudanarwa a yankin na Adamawa, ranar Litinin. Ya ce shugaban Kamaru, Paul Biya, ya nemi ya tabbatar an tura sojoji don kare al’ummomin da suka karbi bakuncinsu da kuma mutanen da suka rasa muhallinsu yayin da ake fadan a Afirka ta Tsakiya
"Rukunin Mbere ya raba fiye da Kilomita 160 na kan iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya [C.A.R.] kuma tare da wannan 'yan tawayen kan iyaka suna kutsawa [suna hayewa zuwa) yankinmu, suna satar shanu," in ji Boukar. "
Mun zo ne don karfafa karfin doka da oda [sojoji], don karfafawa jama'a su kasance cikin shirin tare da sanar da shugabannin (gwamnati) halin da ake ciki a wannan iyakar.
Boukar bai fadi adadin sojojin gwamnati da aka tura domin dakatar da 'yan tawayen ba. Ya dai ce sojojin sun kwace makamai da 'yan tawayen suka shigo da su ba bisa ka'ida ba zuwa Kamaru.
Kamaru ba ta bayar da alkaluma kan adadin shanun da ‘yan tawayen suka karba ba.