Kungiyar Matasan Najeriya U-23 Zasu Nemi Lashe Kofin Gasar Wasan Afirka

Samson Siasia

Babban kochin kungiyar matasa ‘yan kasa da shekaru 23 Samson Siasia, yace yana son lashe gasar kwallon kafa da za’a yi, ta wasannin kasashen nahiyar Afirka, wadda aka shirya yi Brazzeville babban birnin tarayyar Congo.

Kungiyar Najeriya dai na cikin rukuni ‘daya da kasar Sanigal da Ghana a rukuni na B.

Samson Siasia yace kungiyar sa zata fafata ne domin ganin ta samu lashe kofin gasar, ya kuma tabbatar da cewa zasu yi duk abinda ya kama domin ganin sun kai ga wannan matsayi. Lashe wasan zai zamanto matakin farko da zai taimakawa kungiyar zuwa wasannin neman shiga gasar wasannin Olympic mai zuwa da za’a yi.

Ya kuma cigaba da cewa munyi shiri na gaske don tunkarar gasar wasannin, babu ja da baya. Duk da yake shirin na mu ba yadda muke so bane, a dalilin rashin hadin kai da sauran kungiyoyin wasa suka yi mana, na hana ‘yan wasa dawowa gida domin wannan gasar, amma duk da haka muna fatan ganin mun tabuka abin kirki a wasannin na Congo.

Daga karshe dai koch din ya kara da cewa mun yi gyara ga matsalar da muke fuskanta ta shigar da kwallo raga, za kuma mu ci gaba da aiki kan ta har sai mun kai ga fagen wasa.