Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Fafata a Wasani 21 Daban Daban


Ayarin ‘yan wasan da zasu wakilci Najeriya, a wasanin motsa jiki karo na goma sha daya na nahiyar Afirka da za’a yi a kasar Congo Brazzaville, sun bar Najeriya.

Ayarin mutane 573, da suka hada da ‘yan wasan da masu kula dasu sun bar kasar ne ta filin jiragen sama na Abuja a jiya.

Darakta janar na hukumar wasani ta kasa Mallam Alhassan Saleh Yakmut, da sakatare janar na hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Dr. Muhammad Sanusi, da wasu mukarrabai ne suka yiwa ‘yan wasan rakiya.

Najeriya, zata fafata a wasani 21, daban daban, kungiyar kwallon kafa na mata Super Falcons, da kungiyar kwallon kafa na maza ‘yan kasa da shekaru 23.

Super Falcons zasu hadu da kasashen Congo Brazzaville da Tanzania da Ivory Coast a rukunin “A” su kuwa ‘yan kasa da shekaru 23, zasu fuskanci kasashen Ghana da Senegal bayan da Egypt ta janye daga wasannin.

XS
SM
MD
LG