Kulob din Manchester United da Real madrid na shirin tunkarar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a kokarin su na warware yarjejeniyar musayar masu tsaron gidan kungiyoyin David De Gea da Keylor Navas.
Baki daya kungiyoyin biyu sun amince da musayar cewa David De Gea zai koma Spain, shi kuma Navas zai koma kungiyar Manchester united.
Amma sai dai sun mika takaddun yarjejeniyar ga hukumar wasan kwallon kafa ta duniya cikin kurarren lokaci.
Kungiyoyin sun ci gaba da nanata cewa sun mika takardun akan lokaci kuma suna ikirarin cewa suna da shaidar da ta tabbatar da mika takardun cikin lokaci wanda yake dauke da tambarin hukumar kwallon kafar.
Duk da haka De Gea bai riga ya fara sa kayan sabuwar kungiyar ba a sakamakon takaddamar da kungiyoyin suka samu tsakanin su da hukumar kwallon kafar, yayin da shi kuma Navas ke shirin komawa sabuwar kungiyar ranar litinin.
Ana sa ran kai karshen yarjejeniyar ranar talata, ko da shike akwai alamun duka kungiyoyin zasu garzaya kotu domin yin sulhu.