KADUNA, NIGERIA - Ma’aikatan na ganin akwai sakaci da rashin kula da biyan hakkokinsu.
Hakan yasa da sanyin safiyar yau Talata kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta NUEE reshen jihar Kaduna ta kori ma’aikata tare da garkame babban ofishin hukumar gudanarwar samar da wutar lantarki ta jihar KAEDCO sakamakon rashin biyan ma’aikatan hakkokinsu.
Kungiyar NUEE dai tace ta dauki wannan matakin ne sakamakon wasu bukatun ma’aikata da ta ce ta dade tana bin hukumar KAEDCO ta biya musu amma abun yaci tura, inda a yanzu turi ta kai bango.
Da yake maida martini kan matakin na NUEE, Shugaban hulda da jama’a na KAEDCO, Abdulaziz Abdullahi yace akwai alkawarin zama da sukayi da kungiyar a Laraba don gabatar musu da matakan da suke dauka don samar da maslaha amma duk da haka suka dauki wannan mataki.
A watan daya gabata ne dai Ministan Lantarki na Najeriya ya sanar da cewa akwai yiyuwar cire tallafin wutar lantarki sakamakon yawan bashin da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki na kasar da ya haura Naira tiriliyon uku.
A halin da ake ciki a Najeriya na matsala da kuma karancin wutar lanatarki, kama daga jihohi harma da birnin tarayyar kasar, inda ake shafe sa’o’i a wasu lokutan ma kwanaki babu wutar lantarki.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5