Koda yake matakin ya haifar da walwala tsakanin al’umma wasu ‘yan kasar ta Nijar na cewa ya zama wajibi hukumomi su dauki matakai daga darasi da aka koya a wannan fanni.
Jihohi 7 daga cikin 8 da ake da su na jamhuriyar Nijar ne ke amfana da wutar lantarkin da kasar ke saye daga Najeriya a karkashin wata dadediyar yarjejeniyar kasuwancin da kasashen 2 suka cimma dalili ke nan matakin katse wutar lantarki a wani bangare na takunkumin kungiyar CEDEAO ya yi tasiri sosai kan rayuwar al’ummar wannan kasa kafin al’amura su fara daidaituwa a cikin daren Laraba wayewar Alhamis inda aka kwana ba tare da dauke wutar ba, wanda kuma wata takaitacciyar sanarwar da a ka bayar ta kafafen sada zumunta ta tabbatar da cewa, an sake jona wayoyin wuta daga tashar makamashi ta birnin Kebbin Najeriya.
Shugaban kungiyar kulawa da rayuwa Hamidou Sidi Fodi mai fafutukar kare hakkin jama’a a fannin makamashi na mai farin cikin ganin wannan rana musamman don azumin watan Ramadan na gabatowa.
Jama’a ta matukar dandani kuda sanadiyar matakin na makwafciyar kasa wato Najeriya , wannan ya sa har yanzu wasu ‘yan kasar ta Nijar ke nuna fushinsu kan abinda ya faru a tsawon watannin da suka shige.
Jamhuriyar Nijar na da dimbin albarkatun da idan aka sarrafa za su bada damar samar wa jama’arta wadatar makamashi kamar haske rana da iska da ruwan kogin kwara. hambararriyar gwamnatin kasar ta kafa tashar samar da wutar lantarki da hasken rana mai karfin megawatt 30 ba ya ga wasu tashoshin na tunfil azal da ke samar da wuta da injin amma ba ta wadatar ba saboda haka ‘yan kasar ke ankarar da hukumomi cewa, abubuwan da suka faru a tsawon watanni 7 na baya sun isa a koyi darasi.
A washegarin barkewar dambarwar da ta taso bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, hukumomin mulkin soja da wasu kamfanonin gwamnati da masu zaman kansu sun maka CEDEAO a kotu akan bukatar ta dage takunkumin kan wutar lantarki ganin yadda abin ya ja masu asarar dimbin kudaden shiga, sai dai kotun ta yi watsi da wannan bukata, ta na mai cewa ba su da hurumi da hallaci tsoma bakinsu a wannan sha’ani.
Kungiyar ECOWAS a zamanta na 24 ga atan fabreru ta ce ta dage takunkumin ne saboda dalilai na jinkai.
Saurari rahoton :
Dandalin Mu Tattauna