Tsohon Ministan lantarki da kuma Shugaban kamfanin Ferfesa Barth Nnaji ne ya shaida wa Muryar Amurka hakan, tare da cewa aikin zai lashe kimanin dala miliyan dari takwas ($800m).
Farfesa Nnaji ya kara da cewa, “Aikin zai yi tasirin gaske, saboda an tsara aikin ne don samar da ingantacciyar wutar lantarki ga birnin Aba da kananan hukumomi 9 na jihar Abia, masu fadin fili kimanin murabba’in kilomita 4000, da yawan jama’a sama da miliyan ukku. Aikin zai farfado da masana’antu da dama, da kuma tada komadar tattalin arzikin yankin kudu maso gabas.”
A nashi bayanin, kakakin kamfanin C Don Adinuba, “Muna amfani ne da injin turbin hudu daga General Electric, wanda shi ne kamfani mafi girma a duniya a sarrafa kayayyakin lantarki. Abin da yankin Aba ke bukata shi ne kimanin megawatt 100 don inganta harkokin kasuwanci, da yake akwai manyan masana’antu a Aba da ke kashe makudan kudi wajen samun wutar lantarki. Yanzu da shigowar mu, zasu rika samun wutar lantarki daidai gwargwado don raya harkokin su.”
Adinuba ya kara da cewa tashar zata taimaka sosai wajen rage tsadar sarrafa kayayyaki a yankin Aba, tare da rage tsadar kayayyaki ta yadda al’ummar Najeriya baki daya zasu amfana.
Tuni gwamnatin jihar Abia ta yi marhabin da aikin, tare da kamanta shi a matsayin wanda zai kawo muhimmin sauyi a lamuran jihar.
“Wannan ya yi ma’ana sosai, saboda al’ummar mu sun dade suna fama da karancin wuta, musamman a yankin Aba. Kuma da zarar tashar ta fara aiki, masana’antu da yawa zasu farfado,” inji kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Okey Kanu.
Yanzu masana na ci gaba da kamanta wannan aikin Geometric Power Plant a matsayin jari mafi girma a duk kudu maso gabashin Najeriya, kuma ana sa ran cewa shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da tashar a ranar Litinin mai zuwa.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna