Kungiyar Limaman Addinin Musulunci ta Sojoji Ta Tallafawa 'Yan Gudun Hijira dake Maiduguri

Wasu 'yan gudun hijira dake Maiduguri jihar Borno

Wani sashen addinin musulunci na dakarun sojojin Najeriya dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Maiduguri jihar Borno.

Kungiyar limaman ta tallafawa 'yan gudun hijiran da kayan abinci.

Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta yi tattaki zuwa sansanin 'yan gudun hijirar a birnin Maiduguri

Kanar Shehu Mustapha shi ne shugaban kungiyar duk limaman dake barikokin sojojin Najeriya a duk fadin kasar ya yi jawabi a sansanin inda ya soma da matasan dake sananin.Idan suna da wani labari na mutane da zasu kawo ta'adanci ya kamata su sanarda mahukunta ba tare da bata lokaci ba domin a dauki matakan da suka dace.

Sun kawowa masu gudun hijiran kayan masarufi ne domin su nuna damuwarsu da halin da 'yan gudun hijiran ke ciki.

Bayan an mika masu kayan Muryar Amurka ta tambayi wadanda suke cikin sansanin yadda suka ji da tallafin. Kamar yadda ake zato duk sun nuna godiyarsu da fatan Allah ya sama limaman albarka. Sun kuma bayyana irin matsalolin da suke fuskanta a sansanin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Limaman Sojoji Ta Tallafawa 'Yan Gudun Hijira dake Maiduguri - 3' 31"