Cututukan sun hada da cutar amai da gudawa ko kwalara da cutar kyanda da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da suka hada da kananan yara.
An samu barkewar cututukan ne 'yan makonni da suka gabata sakamakon matsalar rashin tsafta da aka samu.
Hukumomin kiwon lafiya da gwamnatin jihar sun tashi haikan sun yaki cututukan.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA yankin arewa maso gabas Alhaji Muhammad Kanar ya shaidawa manema labarai cewa yanzu an magance matsalolin.
Yace an fara samun barkewar cutar kwalara ne da ta yi sanadiyar mutuwar wasu a sansanin amma Allah ya sa akwai 'yan majalisar dinkin duniya dake kula da harkokin kiwon lafiya tare da hukumomin kiwon lafiya na Borno da gwamnatin tarayya duk aka hada kai aka shawo kan cututukan..
Alhaji Kanar yace barkewar cututukan ba zata rasa nasaba da wasu 'yan gudun hijiran dake shigowa daga wasu garuruwa musamman garuruwan kasashen ketare. Yayi misali da wadanda suke fitowa daga wani yanki na kasar Kamaru da basu samun allurorin maganin rigakafi, su da 'ya'yansu. Cikinsu ne aka samu masu cutar kyanda.
Wata matsala kuma ita ce ta saurin cikar matsugunonsu wadanda sun kai dari da wasu 'yan kai. Sukan cika cikin makwanni biyu. Lamarin ya kan kure wadanda suke kwashesu. Kafin su gama wani sansani sai wani daban ya cika. Ko a cikin Maiduguri kawai 'yan gudun hijira wajen miliyan daya ne da dubu dari biyar ne.
Cikin wata daya kusan karin 'yan gudun hijira dubu hudu aka samu.
A karshen wannan watan za'a sake bude makarantun 'yan gudun hijiran.
Ga karin bayani.