Kungiyar IZALA ta Kira Jami'an Tsaro da su Inganta Harkokin Tsaro

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, ko IZALA, a takaice, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Bayan ta kammala taronta na shekara-shekara na ashirin da daya a Jos jihar Filato kungiyar IZALA ta kira jami'an tsaro da su inganta harkokin tsaro da kuma kiran gwamnatin tarayya ta bari 'yan kasar su zabi wanda suke so a zabe mai zuwa.
Kungiyar IZALA ta kira jami'an tsaron Najeriya da su inganta harkokin tsaro a kasar musamman a arewa. Ta kuma kira gwamnatin tarayya ta ba kowane dan kasar 'yancin zaben duk wanda yake so a zaben 2015.

Taron na shekara-shekara shi ne na ashirin da daya. Taken taron shi ne "Gudanar Da Kasaitaccen Zabe Shi Ne Sinadarin Shugabanci Mai Dorewa".

Shugaban majalisar malamai ta kungiyar na kasa Sheikh Muhammed Sani Yahaya Jingir ya bayyana wasu abubuwa da aka tatauna a musabakar ta bana. Yace manufar taron shi ne dada yayatawa da isar da ilimi na Musulunci a faggen rayuwa gaba daya. Akwai mahimmanci na zaman lafiya sabili da haka suke anfani da taron wajen shiryar da malaman tafsiri da fuskantowar watan Ramadana. Malaman ana bukatarsu su je su yada mahimmancin zaman lafiya yadda za'a bunkasa ilimi da tattalin arziki.

Ganin yadda zabe ya karato kungiyar ta sa taken dake da nasaba da siyasa a zabi shugabannin da suka cancanta masu damuwa da damuwar al'umma kuma su kira 'yan majalisu gaba daya cewa fa an zabe su ne domin kwalliya ta biya kudin sabulu. Yakamata su damu da damuwar al'umma.

An kuma kira masu shari'a a kasar cewa duk kasar da bata hukunta masu laifuka ba zata cigaba ba ko kiyaye zaman lafiya.

Ga cikakken rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar IZALA ta Kira Jami'an Tsaro da Sun Inganta Harkokin Tsaro - 5'24"