Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bom ya Fashe da Yammacin


Wani bom da ya fashe da yammacin jiya Talata a inda jama'a suka taru su na kallon wasan gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ya halaka mutane 21 a kalla a garin Damaturu, jahar Yobe.

Shaidu da likitoci sun fada Larabar nan cewa a kalla mutane 27 sun ji ciwo a lokacin da bom din ya tashi.

Dimbin jama'a ne suka taru a wani wurin kallo a Damaturu domin su ga wasan kwallon da aka yi tsakanin Brazil da Mexico a irin talbijin din nan masu fadi da ake mannawa a bango. Shaidu sun ce a cikin wata motar a daidaita sahu aka boye bom din, da ya fashe jim kadan da fara wasan.

Babu mahalukin da ya fito ya dauki alhakin kai harin.

Damaturu ne babban birnin jahar Yobe, daya daga cikin yankunan arewa maso gabashin Najeriya da ke cikin dokar ta baci saboda bala'in hare-haren da 'yan ta'addan kungiyar boko haram ke kaiwa.

A makon jiya hukumomin jahohin Adamawa da Filato suka bada umarnin rurrufe irin wadannan wuraren kallon wasan kwallon kafa saboda gudun yiwuwar kai musu hare-hare.

'Yan ta'addan boko haram sun halaka dubban jama'a a cikin shekaru biyar din da suka yi su na ta kai hare-hare kan makarantu, da Masallatai, da Majami'u, da tashoshin mota da kuma sauran wuraren da jama'a ke taruwa.
XS
SM
MD
LG