Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Ministar Kudin Najeriya ta Ziyarci Jihar Borno


Dr Ngozi Okonjo-Iweala ministar kudin Najeriya
Dr Ngozi Okonjo-Iweala ministar kudin Najeriya

Tawagar ministar kudin Najeriya da ta kunshi tsohon firayim ministan Biritaniya ta kai ziyara Borno akan shirin inganta ilimi da harkokin tsaro.

Yayin da yake karbar tawagar ministar kudin Najeriya Dr. Ngozi Okonjo-Iweala yace gwamnatinsa ba zata bari dalibai su cigaba da zama a gida ba sabili da rufe makarantunsu sanadiyar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa.

Tawagar ministar ta kunshi tsohon firayim ministan Biritaniya Gorden Brown da kuma wasu 'yan kasar Biritaniya. Sun ziyarci jihar Bornon ne domin shirin nan da Biritaniya keyi na inganta ilimi da tsaro a Najeriya musamman a jihohin arewa maso gabas dake fama da rikicin Boko Haram. Shirin zai fi bada karfi ne a jihohin dake cikin dokar ta baci, wato, Adamawa, Borno da Yobe.

Bayan isowar tawagar cikin garin Maiduguri fadar gwamnatin Borno Gorden Brown da babban daraktan samar da agaji na kasa Alhaji Sani Sidi sun ziyarci makarantar firamare inda aka tara dubban 'yan gudun hijira da suka fito daga kauyuka da dama sakamakon irin hare-haren da 'yan Boko Haram suka haddasa.

Daraktan samar da agajin gaggawa Alhaji Sani Sidi ya shaidawa ministar Dr. Ngozi Okonji-Iweala cewa suna da 'yan gudun hijira a wannan sansanin fiye da mutane dubu biyu. Yace sun sama masu kayan abinci da wadanda suke bukata na yau da kullum domin tallafawa rayuwarsu. Banda wadanda ke makarantar firamaren, daraktan yace suna da wasu sassa daban-daban inda suke da 'yan gudun hijira da suke kula da su.

Ministar, Ngozi Iweala, tace sun kawo ziyara ne su tallafa masu kuma su nuna masu cewa shugaba Jonathan yana tare da su.

Wasu 'yan gudun hijirar dake sansanin sun shaida ana kula da su, ana basu abinci da ruwa da makamantansu.

Daga bisani tawagar da gwamnan jihar sun zagaya makarantun da aka kone inda ministar kudin tayi alkawarin tallafawa jihar akan harkokin ilimi da tsaro.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG