Akan haka ne ministan watsa labarai na Najeriya Mr Labaran Maku yace gwamnatin kasar ta damu kwarai da gaske dangane da irin yadda ake yada manufofi na kabilanci da bangaranci game da aikin jam'an tsaro.
Kowane dan Najeriya nada 'yancin yayi walwala a koina a kasar amma kuma tilas ne a dauki matakan tsaro idan akwai barazana. Yace matsalar kasar itace abu kadan sai a kawo kabilanci da bangaranci ciki. Yace sati biyu da suka wuce wani gwamnan arewa yace kungiyar Boko Haram na kokarin kai hare-hare a kudancin kasar.
Dangane da wai 'yan Boko Haram ba zasu tafi wani wuri a cikin jerin gwanon motoci ba sai ministan yace mutum ba zai sani ba domin suna iya badda kamanni.
Da yake mayarda martani dangane da matakin da jami'an tsaro suka dauka Dr Bashiru Kurfi shugaban kungiyar dake fafitikan kare hakkin Biladama yace sun kammala shirin gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu domin su kalubali gwamnatin. Yace suna son su kare hakkin 'yan arewa Musulmai.
Ga cikakken rahoton Hassan Umar Tambuwal.